logo

HAUSA

Bangaren Sin ya yi kira ga bangarorin dake shafa rikicin Ukraine da su maido da tattaunawa cikin sauri

2024-01-11 11:56:36 CMG Hausa

Kwamitin sulhu na MDD ya gudanar da taro game da rikicin Ukraine a jiya Laraba, inda zaunannen mataimakin wakilin Sin a MDD Geng Shuang ya bayyana cewa, ana habaka rikicin Ukraine, kana batutuwan hare-hare da mace-mace da jikkatar fararen hula sun faru, yanayin jin kai kuma yana ci gaba da tabarbarewa. Yana mai cewa bangaren Sin ya damu matuka game da yanayin da ake ciki. 

Ya ce bangaren Sin ya yi kira ga bangarori masu ruwa da tsaki a rikicin Ukraine da su kwantar da hankulansu, su yi iyakacin kokari wajen bin dokokin jin kai na kasa da kasa, su kare tsaron fararen hula da manyan ababen more rayuwarsu, musamman ma tsaron kayayyakin nukiliya. Yana mai kira ga kasa da kasa da hukumomin jin kai su kara karfin gudanar da aikin ceto, ta yadda za a taimakawa mutanen da rikicin ya shafa.

Geng Shuang ya jadadda cewa, a kan batun Ukraine, bangaren Sin ya dade yana goyon bayan zaman lafiya da tattaunawa. Kuma zai ci gaba da tuntubar bangarorin daban daban, domin ba da gudummawarsa wajen warware rikicin. (Safiyah Ma)