logo

HAUSA

Kasar Sin ta bayar da gudunmuwar tantuna domin ‘yan gudun hijira da wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a Sudan ta Kudu

2024-01-11 14:34:48 CMG Hausa

Kasar Sin ta bayar da gudunmuwar tantuna 8,808 ga gwamnatin Sudan ta Kudu, domin taimaka mata bayar da mafaka ga dubban ‘yan kasar da suka koma gida bayan gujewa rikici a Sudan.

Ministan kula da harkokin jin kai na Sudan ta Kudu, Albino Akol Atak ya bayyana yayin bikin mika kayayyakin da ya gudana jiya a birnin Juba cewa, a watan Mayu 2023, kasar Sin ta bayar da gudunmuwar kayayyakin abinci ga mutanen da suka koma gida da ma wadanda suka rasa matsugunansu. Haka kuma a yanzu, sun karbi wasu karin tallafin tantuna domin taimakawa ‘yan kasar da suka fito daga Sudan da ma wadanda suka rasa matsugunansu a cikin kasar saboda matsalolin jin kai.

Ya kara da cewa, tun bayan barkewar rikici a ranar 15 ga watan Afrilu, gwamnatin Sudan ta Kudu ke fafutukar ganin ta kula da ‘yan kasar dake komawa gida da ma ‘yan gudun hijira na kasar Sudan.

Zuwa ranar Litinin, Sudan ta Kudu ta karbi mutane 489,284 daga Sudan, kuma kimanin kaso 82 daga cikinsu, ‘yan asalin kasar ta Sudan ta Kudu ne. (Fa’iza Mustapha)