Kasashen Sin da Saliyo sun yi alkawarin hada gwiwa domin yaki da cututtuka masu yaduwa
2024-01-11 13:54:03 CMG Hausa
Kasashen Sin da Saliyo sun lashi takobin karfafa hadin gwiwa wajen kandagarki da takaita yaduwar cututtuka domin inganta lafiyar al’ummar Saliyo.
Cibiyar kandagarki da takaita yaduwar cututtuka ta Sin wato China CDC da ma’aikatar kula da lafiya da tsafta ta Saliyo, sun gudanar da wani taron karawa juna sani jiya Laraba a birnin Freetown, kan sabbin cututtuka masu bullowa da wadanda ke sake bullowa bayan shawo kansu. Taron ya hada masana da masu bincike da kwararrun ma’aikatan lafiya da masu tsara dabaru a bangaren kiwon lafiya.
Xu Jianguo, malami a kwalejin nazarin Injiniya na kasar Sin dake aiki a cibiyar CDC ta kasar ya ce, manufar taron ita ce, karfafa hadin gwiwa da shiryawa da tunkarar kalubalen lafiya masu bullowa, yana mai cewa, taron na da nufin bayar da gudunmuwa ga kokarin da ake na takaita yaduwar cututtuka a Saliyo, wanda daga bisani zai inganta lafiyar al’ummar kasar.
Xu Jianguo ya kuma jaddada dadaddiyar abota da hadin gwiwa dake tsakanin Sin da Saliyo a fannin kiwon lafiyar al’umma, musamman a lokutan da aka yi fama da barkewar cututtukan Ebola da COVID-19 a Saliyo.
A nasa bangaren, mukaddashin ministan lafiya na Saliyo Charles Senessie, ya ce karuwar cuttuka kamar na zazzabin Lassa a kasar ya jaddada bukatar da ake da ita na samun ingantaccen tsarin kiwon lafiya da tsare-tsaren sa ido da matakan kandagarki domin dakile yaduwarsu.
Ya kara da cewa, kyakkyawan hadin gwiwa tsakanin Saliyo da abokan hulda na kasashen waje, ciki har da Sin, zai karfafa karfin kasar na yaki da cututtuka. (Fa’iza Mustapha)