logo

HAUSA

Najeriya za ta goyi bayan yarjejeniyar ciniki ba tare da shinge ba tsakanin kasashen dake nahiyar Afrika

2024-01-11 13:57:30 CMG Hausa

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta kara tabbatar da kudurinta na mara baya ga yarjejeniyar cikini mara shinge tsakanin kasashen dake nahiyar Afrika a matsayinta na kasa mafi yawan al’umma da yalwar tattalin arziki.

Shugaban hukumar kwastam ta kasa Mr Bashir Adewale Adeniyi ne ya tabbatar da hakan a ranar Laraba 10 ga wata yayin wani taron manema labarai a birnin Abuja.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

Shugaban hukumar ta kwastam a tarayyar Najeriya ya ci gaba da cewa, ya zama wajibi Najeriya ta yi aiki da wannan yaejejeniya musamman idan aka yi la’akari da yawan masana’antun dake kasar, inda ya ce, tun bayan kulla wannan yarjejeniya a watan Oktoban 2022, sama da kasashe 30 ne suke aiki da yarjejeniyar.

Mr. Bashir Adewale Adeniyi ya ce, batun tabbatar da nasarar ciniki mara shinge tsakanin kasashen dake nahiyar Afrika yana daya daga cikin muhimman abubuwan da hukumar kwastam za ta baiwa fifiko cikin wannan sabuwar shekara, baya ga zamanintar da aiyukan hukumar da inganta tsarin lura da kan iyakoki da kuma horas da ma’aikata.

A kan batun kudaden shigar da hukumar kwastam din ta tara kuwa a shekarar bara ta 2023, Mr Bashir Adewale Adeniyi ya ce,

“Adadin kudin shigar da aka tara ya kai naira tiriliyon 3 da biliyan dari 2 da 6 da miliyan dubu dari 6 da 3 da dubu 417 da naira 315 da kuma kwabo 47, kuma wannan adadi shi ne irinsa na farko a tarihin kafuwar hukumar da aka taba tarawa, sannan kuma a yawan kudaden da ake tarawa a duk wata shi ma dai an samu ci gaba sosai.”

Haka kuma hukumar ta kwastam ta tarayyar Najeriya ta sha alwashin tara naira tiriliyan 5.79 zuwa karshen wannan shekara ta 2024 kamar yadda gwamnati ta kayyade mata karkashin manufofin raya harkokin tattalin arzikin kasa. (Garba Abdullahi Bagwai)