logo

HAUSA

Sana’ar jigilar sakwanni ta kasar Sin ta shaida ma duniya bunkasuwar tattalin arzikin kasar

2024-01-11 16:34:45 CMG HAUSA

DAGA MINA

Abokai, ni ce MINA, da fatan za ku biyo ni don mu duba yadda sana’ar jigilar sakwanni ke gudana a nan kasar Sin.

  Duk wani sako na iya zama wani abu ne da aka saya ko aka sayar, wanda ya bayyana wadatar sana’ar samar da kayayyaki da kasuwanni. Shekaru 3 a jere ne, wato daga shekarar 2021 zuwa ta 2023, yawan sakwanin da aka yi jigilarsu a nan kasar Sin ya zarce biliyan 100, har ma wannan adadi ya zarce biliyan 130 a shekarar 2023, adadin da ya kai kashi 63% na dukkan sakwannin da aka yi jigilarsu a duniya a shekarar 2022, kuma ya ninka sau 5.5 bisa na Amurka, yayin da ya ninka sau 13.3 bisa kan na kasar Japan, sai kuma sau 23.5 kan na Birtaniya. Wannan adadi ya ba ni mamaki matuka, wanda ya alamanta cewa, Sin ta zama jagorar sana’ar yin jigilar sakwanni a duniya.

  Yawan karuwar adadin ya kuma zama wani bangaren dake bayyana farfadowa da kuma bunkasuwar tattalin arzikin Sin, wanda ya shaida ma duniya kuzarin kasuwanninta da boyayyen karfin sana’ar jigilar sakwannin kasar, yayin da hasashen da ake kan makomar tattalin arzikin Sin mai haske bai sauya ba.

  Ban da ingancin bunkasuwar sana’ar, aikin jigilar sakwanni na da sauri a kasar, ga shi yanzu haka kayan da na saya, ya iso cikin mintuna Talatin kawai. (Mai tsara bidiyo da rubutu: MIN)