logo

HAUSA

Tattalin arzikin yankin Afirka dake kudu da hamadar Sahara ya karu da kaso 2.9 a 2023

2024-01-10 10:37:48 CMG Hausa

Cikin sabon rahotonsa, Bankin Duniya ya ce tattalin arzikin yankin Afrika dake kudu da hamadar Sahara ya karu da kaso 2.9 a shekarar 2023, idan aka kwatanta da kaso 3.7 na shekarar 2022.

Rahoton da bankin ya fitar jiya Talata mai taken Hasashen Tattalin Arzikin Duniya, ya bayyana cewa, ci gaban tattalin arziki a manyan kasahsen yankin 3 da suka hada da Nijeriya da Afrika ta Kudu da Angola, ya ragu zuwa kaso 1.8 kan matsakaicin mataki a bara, lamarin da ya rage karfin tattalin arzikin nahiyar Afrika baki daya.

Farfadowar tattalin arziki bayan annobar COVID-19 ya gamu da tafiyar hawainiya saboda raguwar bukatu daga waje da kuma tsauraran manufofin da aka dauka a cikin gida domin shawo kan ci gaba da hauhawar farashin kayayyaki.  

Bankin ya yi hasashen cewa, ana sa ran ci gaban tattalin arzikin Afrika zai farfado zuwa kaso 3.8 a bana, kana ya karu zuwa kaso 4.1 a shekarar 2025, yayin da matsin hauhawar farashin kayayyaki ya ragu kana sharuddan hada-hadar kudi suka yi sauki. (Fa’iza Mustapha)