Sin ta yi kira ga tsagaita bude wuta a zirin Gaza
2024-01-10 10:39:47 CMG Hausa
Mataimakin zaunannen wakilin Sin dake MDD Geng Shuang ya bayyana a jiya cewa, kasar Sin tana kira ga kasa da kasa da su yi namijin kokari tare wajen sa kaimi ga tsagaita bude wuta a zirin Gaza cikin hanzari.
Geng Shuang ya bayyana game da batun yin amfani da kujerar na ki a babban taron MDD cewa, rikici tsakanin Palesdinu da Isra’ila a wannan zagaye ya shafe fiye da watanni 3, inda ake fama da matsalar jin kai a zirin Gaza, kana fararen hula na rasa rayukansu a kowace rana, yayin da yanayin ke kara tsananta.
Ya ce kasa da kasa sun yi kira da a tsagaita bude wuta nan da nan a zirin Gaza. Yana mai cewa wannan ne tushen maido da zaman lafiya a yankin. Amma har yanzu, kwamitin sulhu na MDD bai cimma daidaito kan kiran tsagaita bude wuta a zirin Gaza ba. Ya ce Sin tana bakin ciki da yadda kasar Amurka ta sake yin amfani da kujerar na ki wajen nuna kin amincewa a yayin taron da kwamitin sulhu ya shirya a ranar 22 ga watan Disamban shekarar bara game da wannan batu.
Geng Shuang ya bayyana cewa, ana bukatar tsagaita bude wuta nan da nan don ceto rayukan fararen hula, da magance tashe-tashen hankula a yankin, da kuma tabbatar da shirin kafa kasashe biyu. Bugu da kari, ya ce kasar Sin za ta ci gaba da yin kokari tare da kasa da kasa wajen sa kaimi ga kwamitin sulhun da ya sauke alhakin dake wuyansa da aiwatar da ayyukan kawo karshen rikicin zirin Gaza da kuma samun zaman lafiya da na karko a yankin gabas ta tsakiya. (Zainab Zhang)