logo

HAUSA

Gwamnatin jihar Jigawa ta samar da kwamitin kwato makiyayu da burtalai da wasu suka mallake ba bisa ka`ida ba a jihar

2024-01-10 09:19:52 CMG Hausa

A wani mataki na kawo karshen yawan rikice-rikice tsakanin manoma da Fulani makiyaya, gwamnatin jihar Jigawa dake arewacin Najeriya ta samar da kwamiti na musamman da zai kwato makiyayu da burtalai da wasu tsirarun mutane suka mallake ba bisa ka’ida ba a sassan jihar.

Babban sakataren hukumar sassanta tsakanin manoma da Fulani makiyaya ta jihar Jigawa Dr. Salisu Abdullahi ne ya tabbatar da hakan yayin kaddamar da shirin allurar riga-kafin dabbobi na shekara ta 2023/2024 da ake kira da Huji wanda kuma da aka gudanar a karamar hukumar Ringim.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi bagwai ya aiko mana da rahoto. 

Dr. Salisu Abdullahi ya ce, da jimawa gwamnati ta gano cewa son zuciya da wasu suka nuna wajen mamaye filayen kiwo da kuma na noma ta haramtacciyar hanya yana taka rawa sosai wajen samun rigingimu tsakanin manoma da Fulani makiyaya a jihar baki daya. 

Ya ce, rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma yana daya daga cikin kalubalen tsaro da jihar ke fuskanta, amma aikin da kwamitin yake yi yana tasiri sosai wajen raguwar fitintunu tsakanin Fulani makiyaya da manoma.

“Bayan wannan hujin dabbobi, akwai abubuwa da yawa da wannan gwamnati ta shirya domin samun zaman lafiya tsakanin wadannan mutane guda biyu, daman manomi da makiyayi ’yan uwa ne. Batun yanzu ba kawai wani abu ne yake faruwa kamar dai yadda Bahaushe ke cewa harshe da hakori ma ana sabawa. Wannan hujin dabbobi da aka kaddamar yana daga cikin abubuwan da wannan gwamnati ta tanada domin a samu zaman lafiya dauwamamme tsakanin wadannan mutane biyu. Akwai kuma wani kwamiti da wannan gwamnati ta kafa na kwato makiyayu da burtalai na manoma wanda aka bayar da su ba bisa ka’ida ba, wanda shi ma muna ganin yana daya daga cikin abubuwan da suka sanya aka samu zaman lafiya tsakanin wadannan mutane guda biyu.”

Kasancewar an dauki shekaru ba a gudanar da shirin riga-kafin hujin dabbobi ba a jihar ta Jigawa ya sanya wasu Fulani bayyana farin cikinsu.

“Shekara da shekaru an jima tun lokacin gwamnatin Sule Lamido ba a gudanar da wannan allura ba, In sha Allah irin wadannan abubuwa za su kara tabbatar da zaman lafiya.” 

“Mun yi farin ciki dari bisa dari ga gwamnatin jihar Jigawa, domin ba abin da za mu ce mata sai dai mu yi mata godiya domin ta karrama Fulanin jihar Jigawa, kuma ta dauki wannan abu ta kawo shi nan yankin karamar hukumar Ringim domin a kaddamar da shirin a jiha baki daya.” (Garba Abdullahi Bagwai)