logo

HAUSA

Idan Kana da Kyau

2024-01-10 15:50:29 CMG HAUSA

DAGA Ibrahim Yaya

A yayin da al’ummar Sinawa a duk fadin duniya ke shirye-shiryen bikin bazara na wannan shekara, bikin gargajiya mafi kasaita ga al’ummar Sinawa, ko kuma bikin sabuwar shekara bisa kalandar gargajiyar kasar Sin, a hannu guda kuma hukumar kula da sufurin jiragen saman fasinjoji ta kasar Sin, ta ce wannan sashe na sa ran samun tafiye-tafiye miliyan 80 na fasinjoji yayin bikin sabuwar shekarar gargajiyar kasar dake tafe.

A cewar hukumar, wannan adadi ya kai karuwar kaso 44.9 idan aka kwatanta da makamancin lokacin a bara, kuma ya kai karuwar kaso 9.8 a kan wanda aka samu a makamancin lokaci na shekarar 2019.

Bayanai na nuna cewa, a bana tsawon lokacin tafiye-tafiyen zai kai har kusan kwanaki 40, wato daga ranar 26 ga watan Junairu zuwa 5 ga watan Maris.

A don haka, ana sa ran gudanar da a kalla tafiye-tafiye da bai gaza miliyan 2 ta jiragen sama ba a kullum, inda ake sa ran jirage da ba su gaza kimanin 16,500 za su rika tashi a kullum.

Domin biyan bukatun al’ummar kasar a fannin tafiye-tafiye yadda ya kamata, ita ma hukumar kula da jiragen kasa ta kasar ta bayyana cewa, za ta fara aiki da wani sabon shirin gudanar da layin dogo, daga ranar 10 ga watan Janairun shekarar 2024, da nufin inganta karfin jigilar kayayyaki da ma fasinjoji.

A karkashin sabon shirin, za a kara sabbin jiragen kasa na fasinja guda 233 a fadin kasar, wanda ya kawo jimillar adadinsu zuwa 11,149. Jimillar jiragen kasa na jigilar kayayyaki guda 22,264 ne za su rika aiki a fadin kasar, bayan shirin ya fara aiki, karuwar jirage 40, idan aka kwatanta da tsarin da ake amfani da shi a halin yanzu.

Wannan ya kara nuna cewa, duk da managartan hanyoyin sufuri na zamani da gwamnati ta samar a sassan kasar, a lokaci guda kuma, tana kokarin kara inganta su, ta yadda za su dace da zamani tare da biyan bukatun al’ummar kasar a duk lokacin da bukatar hakan ta taso, matakan da ya dace kasashe su yi koyi da su, don sauke nauyin dake bisa wuyansu na bautawa jama’a. Wai idan kana da kyau to ka kara da wanka. (Ibrahim Yaya)