Yadda Sin take kokarin bunkasa tattalin arzikinta tare da ragowar sassan duniya
2024-01-10 09:38:52 CMG Hausa
A yayin da kasar Sin take kokarin samun ci gaba mai inganci, a hannu guda kuma tana fadi-tashin fadada matakai da ka’idojin da suka shafi manufar kasar ta kara bude kofa ga ketare, da inganta matakan hadin gwiwar cinikayya da zuba jari.
A karkashin manufar, kasar Sin ta samu ci gaba mai inganci. Sin ta saukaka jerin matakan shiga kasuwannin kasar, ta yadda kamfanonin ketare za su ci gajiyar kyawawan muhallin kasuwanci a kasar.
Haka kuma kasar Sin na kara zage damtse wajen samar da kyakkyawan yanayin kasuwanci bisa doka wanda ya yi daidai da mizanin kasa da kasa. Duk da karuwar rarrabuwar kawuna a harkokin tafiyar duniya da ra’ayin bayar da kariya ga harkokin cinikayya da wasu kasashe ke yi, kasar Sin ta himmatu wajen kara bude kofofinta ga kasashen ketare, a wani mataki na kara janyo jarin waje da samar da karin damammaki ga ’yan kasuwan ketare.
A matsayinta na kasa ta biyu mafi karfin tattalin arziki a duniya, kana kasar dake kan gaba a fannin cinikayya a duniya, kasar Sin ta bayyana kudurnta na kara bude kofofinta da ma shirinta na samun ci gaba mai inganci da kara samar da damammaki ga duniya.
Bayanai na nuna cewa, a shekarar da ta gabata, tattalin arzikin kasar Sin ya jure matsin lamba daga waje, ya ci gaba da farfadowa, tare da samun ci gaba mai inganci. Bayanai sun tabbatar da cewa, tushen tattalin arzikin kasar Sin, mai cike da kwanciyar hankali da inganci cikin dogon lokaci, bai sauya ba, kasashen duniya na kara amincewa da tattalin arzikin kasar Sin a wannan shekara. Haka kuma kasar Sin za ta ci gaba da kasancewa wani muhimmin injin din ci gaban tattalin arzikin duniya a sabuwar shekara, da samar da tabbaci da ginshiki mai inganci ga tattalin arzikin duniya mai cike da rashin tabbas. (Ibrahim Yaya, Fa’iza Mustapha/Sanusi Chen)