logo

HAUSA

Gwamnatin Najeriya za ta gina kananan makarantun sakandire na koyon sana’o’in hannu

2024-01-09 10:01:03 CMG Hausa

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta fara aikin gina kananan makarantun sakandare na musamman da za su rinka bayar da horo kan sana’o’in hannu ga matasa a jihohin 36 dake kasar.

Ministan ilmi Farfesa Tahir Manman ne ya tabbatar da hakan a jihar Adamawa lokacin da yake duba aikin ginin makarantar da aka samar a harabar kwalejin Janaral Murtala Muhammad dake Yola, fadar gwamnatin jihar.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

Ministan ilmin na tarayyar Najeriya ya ce, samar da irin wadannan makarantu yana daga cikin manufar gwamnati ta samar da al’ummar da take da fasahar dogaro da kai, inda ya ce, daukar wannan mataki zai kawo karshen kalubalen dake haifar da tafiyar hawainiya wajen ci gaban bangaren ilmi a Najeriya.

Farfesa Tahir Manman ya yaba matuka bisa yadda aikin kwangilar ginin makarantar ke gudana karkashin kulawar hukumar ilmin bai daya ta kasa, wanda aka bayar da aikinsa a kan naira miliyan dari 2.

“Wannan aiki, makaranta ce ta bayar da horon sana’o’in hannu, makaranta ce da tsarinta ya sha bamban da na sauran makarantun sakandare, karamar sakandare ce da za ta mayar da hankali wajen baiwa dalibai horo a kan kwarewa a wasu fannonin sana’o’i.”

Ministan ya ce, kamar yadda aka tsara dai a irin wadannan makarantu da za a samar kowanne dalibi yana da damar zabar fannin da yake son samun horo a kai a iya shekarun karatun karamar sakandare.

Dan kwangilar da yake gudanar da aikin, ya tabbatarwa ministan cewa zuwa karshen wannan wata na Janairu zai kammala aikin. (Garba Abdullahi Bagwai)