logo

HAUSA

Shugaban Nijeriya ya dakatar da minista bisa zargin badakalar kudi

2024-01-09 10:05:33 CMG Hausa

Shugaban Nijeriya Bola Tinubu, ya dakatar da ministar harkokin jin kai da yaki da fatara ta kasar Betta Edu, bisa zargin wata badakalar kudi da ofishinta ya aiwatar.

Wata sanarwa da kakakinsa Ajuri Ngelale ya fitar jiya, ta ce dakatarwar ta fara aiki ne nan take, domin ba hukumar yaki da cin hanci ta kasar damar gudanar da bincike.

Sanarwar ta kara da cewa, wannan mataki ya yi daidai da kudurin shugaban na tabbatar da daukaka mutunci da tsare gaskiya wajen tafiyar da arzikin al’ummar Nijeriya.

Betta Edu ta fara shan suka ne bayan an yi zargin ta bada umarnin tura naira miliyan 585.2, kwatankwacin sama da dala 661,374 da aka shirya rabawa jama’ar kasar masu rauni, zuwa wani asusun banki na wani ma’aikacin gwamnati.

Shugaban ya kuma kafa wani kwamiti karkashin ministan kula da tattalin arziki da na harkokin kudi, wanda ya dorawa nauyin gudanar da cikakken bincike kan tsare-tsaren kudi na shirye-shiryen tallafawa al’ummar kasar. (Fa’iza Mustapha)