logo

HAUSA

Sojojin dake mulki a Nijar sun saki dan Mohamed Bazoum

2024-01-09 09:58:42 CMG Hausa

Wata kotun soja a Jamhuriyar Nijar, ta sanar da sakin wucin gadi na Salem Mohamed Bazoum dan tsohon shugaban kasar Mohamed Bazoum a jiya Litinin. Wannan na zuwa ne, bayan daga ziyarar da tawagar kungiyar ECOWAS ko CEDEAO ta yi niyyar kai wa birnin Yamai a ranar 10 ga watan Janairu, da nufin lalubo bakin zaren ricikin siyasar kasar.

Daga birnin Yamai, abokin aikinmu Mamane Ada, ya aiko mana da wannan rahoto. 

A yayin da yake hannun sojoji tare da ma’haifinsa shugaba Mohamed Bazoum da aka cabke bayan juyin mulki a cikin shekarar da ta gabata, dan tsohon shugaban kasa Salem Mohamed Bazoum ya samu sakin talala a ranar jiya Litinin 8 ga watan Janairun shekarar 2024.

A cewar wani matakin kotun soja dake Yamai, Salem ya samu wata takardar shaidar sakin talala daga jujun shigar da kara na kotun soja a ranar 8 ga watan Janairun shekarar 2024 dake kula na ya amsawa kotu da zaran zai yi bukata.

Wannan matakin saki, koda na wucin gadi ne na dan tsohon shugaban kasa, na nuna ko shakka babu wani ci gaba cikin yanayin sulhunta rikicin siyasa da ya girgiza Nijar tare da takunkumin CEDEAO. Kungiyar yammacin Affrika ta tilasta sakin tsohon shugaban kasa Mohamed Bazoum kafin duk wata tattaunawa domin dage takunkumi dake raunata kasar Nijar sosai.

Me zai faru, amsa a ’yan kwanaki masu zuwa game da makomar Mohamed Bazoum da matarsa da kuma abin da kungiyar CEDEAO za ta ce. Ko ma mene ne wannan sanarwa wani babban ci gaba ne kan kokarin daidaita rikicin siyasa bayan juyin mulkin ranar 26 ga watan Yulin shekarar 2023, ko da cewa abin da zai sanya janye takunkumi na ta’allaka da sakin Mohamed Bazoum.

Mamane Ada, sashen hausa na CRI daga Yamai a jamhuriyar Nijar.