logo

HAUSA

Shugabannin kasashen Masar da Falasdinu sun tattauna yanayin da ake ciki a Falasdinu

2024-01-09 11:11:27 CMG Hausa

Shugaban Masar Abdel Fattah al Sisi ya tattauna da takwaransa na Falasdinu Mahmoud Abbas, wanda ke ziyara a Cairo, babban birnin kasar Masar a jiya Litinin. Bagarorin biyu sun tattauna yanayin da ake ciki a Falasdinu, musamman batutuwa irinsu rikicin da ake fama da shi a zirin Gaza.

Shugaban kasar Masar ya ba da sanarwar cewa, ya kamata shugabannin kasashen biyu su jadadda muhimmiyar gudummawar da gwamnatin Falasdinu ta bayar, kuma dole ne a dauki dukkan matakan da suka dace don goya mata baya wajen ba da gudummawarta. 

Bangarorin biyu sun bayyana cewa, batun Falasdinu yana bukatar al’ummar kasa da kasa ta sauke nauyin da ya rataya a wuyansu na tarihi da siyasa da kuma jin kai. Suna masu cewa ta hakan ne za a warware matsalar cikin adalci, wadda ta hada da kafa kasar Falasdinu mai cin gashin kanta bisa iyakar da aka shata a shekarar 1967, kuma gabashin birnin Kudus ya kasance babban birninta.

Shugabannin sun kuma bayyana adawarsu ga duk wani yunkuri na gurgunta harkokin Falasdinu ko kore Falasdinawa daga kasarsu ta kowace hanya. (Safiyah Ma)