logo

HAUSA

Likitocin tawagar ba da agajin likitanci ga kasar Zimbabwe ta kasar Sin sun kawo sabon fata na kiwon lafiya ga fararen hula na wurin

2024-01-09 16:00:05 CMG Hausa

A cibiyar magungunan gargajiya da samar da alluran Acupuncture na Sin dake Zimbabwe, likitocin tawagar ba da agajin likitanci ga kasar Zimbabwe ta kasar Sin, sun kawo sabon fata na kiwon lafiya ga fararen hula na wurin ta hanyar ba da jinyar alluran Acupuncture. A cikin shirin mu na yau, za mu ci gaba da gabatar muku labaran tawagar ba da agajin likitanci ga kasashen waje ta kasar Sin dake gudanar da aikin likitancin Acupuncture a kasar Zimbabwe, tare da sa kaimi ga bunkasuwar ayyukan likitanci na kasar.