logo

HAUSA

Hukumar kwastam ta Najeriya ta saki wata motar dakon kudi da ake amfani da ita wajen fasa kaurin shinkafar waje

2024-01-08 09:05:14 CMG Hausa

Shiyya ta biyu dake jihar Ogun ta hukumar kwastam a tarayyar Najeriya ta saki wata motar dakon kudi mallakin wani banki bisa zargin amfani da ita wajen fasa kaurin shinkafa ’yar waje a yankunan dake kan iyakokin kasar.

Mataimakin kwantrolan shiyya na hukumar Mr. Bisi Alade ne ya tabbatar da hakan yayin wata ganawa da manema labarai a ofishinsa. Ya ce, abun takaici duk da kokarin dakile amfani da shinkafar waje a Najeriya amma wasu bata gari na amfani da dabaru kala-kala wajen kawo cikas ga manufar gwamnati.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

Mataimakin kwantrolan hukumar shiyya ta 2 ya ce, jami’an hukumar suna bakin kokarinsu ba dare ba rana wajen tabbatar da ganin an kawo karshen fasa kaurin kayayyakin da gwamnati ta haramta shigo da su Najeriya.

Ya ce, ya zama wajibi ga hukumar ta tabbatar da manufofin gwamnati ta fuskar wadata kasa da abinci, kuma hakan zai wanzu ne kawai ta hanyar karfafa gwiwar ’yan Najeriya wajen noman abinci a cikin gida tare da dakile yaduwar shinkafa ’yar waje a kasa.

“Hadin gwiwar jami’an wannan hukuma dake sintiri a kan iyakar Oluranda a jihar Ogun sun kama motar dakon kudi dauke da shinkafa ’yar waje da kuma tsabar kudi naira miliyan 22.489 da naira dari 5 a kan hanyar Shokoto-Idon-Doga zuwa Abeokuta.”

Mr Bisi Alade ya ce, an kama motar shekaru 2 da suka gabata, bayan kuma dogon bincike da aka gudanar, yanzu dai an saki motar da mutane uku da ake zargi da hannu, wanda tun a wancan lokaci suke a tsare. (Garba Abdullahi Bagwai)