logo

HAUSA

Equatorial Guinea za ta daukaka huldarta da Sin zuwa wani sabon matsayi, in ji shugaban kasar

2024-01-08 14:05:01 CMG

Shugaban kasar Equatorial Guinea Teodoro Obiang Nguema Mbasogo ya yaba da kyakkyawar rawar da kasar Sin ke takawa a bunkasuwar kasarsa, inda ya ce, kasarsa na nuna cikakken goyon baya ga shawarwarin da kasar Sin ta bayar wajen inganta ayyukan tafiyar da harkokin duniya, kuma za ta yi kokarin daukaka huldar kasashen biyu zuwa wani sabon matsayi.

Shugaban ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi takardar nadin Wang Wengang a matsayin jakadan kasar Sin a Equatorial Guinea.

A jawabinsa Wang Wengang ya ce, Sin da Equatorial Guinea sun cimma manyan nasarori a huldar abokantaka ta hadin gwiwa dake tsakaninsu, kuma Sin za ta yi kokarin karfafa dankon zumunta da hadin gwiwar cin moriyar juna tare da kasar Equatorial Guinea.

Wang Wengang ya isa kasar Equatorial Guinea a ranar 31 ga watan Disamban bara, inda ya fara aiki a matsayin jakadan kasar Sin a kasar.(Lubabatu)