logo

HAUSA

Sin ta yi kira ga bangarori daban-daban a Gaza da su dakatar da bude wuta don kare fararen hula

2024-01-08 20:35:54 CMG HAUSA

 

Yau Litinin, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta bayyana a gun taron manema labarai cewa, bangaren Sin na matukar bakin ciki ga rasuwar ‘yan jarida biyu a zirin Gaza. Ta ce a cikin watanni uku da aka shafe rikicin Falasdinu da Isra'ila, an kashe kusan mutane dubu 23 a zirin Gaza, sannan an kashe 'yan jarida sama da 100. Kasar Sin ta yi kira da babbar murya ga dukkan bangarorin da abin ya shafa, musamman Isra'ila, da su yi taka-tsantsan, tare da aiwatar da kudurorin MDD da suka dace, da tsagaita bude wuta, da kare fararen hula, da kuma kaucewa irin wadannan bala'o'i.

A yayin da take magana kan rikicin Ukraine, Mao Ning ta ce, a ko da yaushe Sin ta yi imanin cewa, tattaunawa da yin shawarwari, ita ce hanya daya tilo da za a iya warware rikicin na Ukraine.

Dangane da wasu matakan da Amurka ta dauka kan kasar Sin kuwa, Mao Ning ta ce, Amurka na ci gaba da kara daukar matakan hana kasar Sin fitar da kayayyaki, bisa dalilan da ta kira wai "tsaron kasa" da kuma dakile kamfanonin da ke sarrafa na'urori na kasar Sin ba tare da dalili ba.

Ban da wannan kuma, game da takardar da Japan da Koriya ta kudu suka bayar, ta ce, Sin na mai da hankali sosai kan batun, a cewarta, yankin Asiya da Pasifik wuri ne mafi zaman lafiya da bunkasuwa, ba dandalin ne na takara ga manyan kasashe ba.

A yayin taron, Mao Ning ta ce, kasar Sin tana son samar da yanayin kasuwanci mai salon bude kofa ga jama'a, da hada kai, da nuna gaskiya, ba tare da nuna wariya ga kamfanoni daga sassan duniya ba, ta yadda za su zuba jari da yin hadin gwiwa a kasar Sin. (Amina Xu)