logo

HAUSA

Labarin Lv Yating game da yadda take raya sana’arta ta samar da kayan fadi-ka-mutu

2024-01-08 19:06:36 CMG Hausa

A cikin 'yan shekarun nan, dalibai 'yan kasar Sin da ke karatu a kasashen ketare da yawa suna zabar komawa kasarsu don ba da gudummawarsu ga ci gaban kasa, tare da tabbatar da burikansu, da kuma kokartawa wajen cimma su. A cikin shirinmu na yau, za mu kawo muku wani labari ne game da yadda wata baiwar Alla mai suna Lv Yating ke raya sana’arta.

Da an shiga cikin kamfanin fadi-ka-mutu na Lv Yating da ke yankin Changnan na garin Jingdezhen, dimbin kayan fadi-ka-mutu na Linglong masu launuka iri-iri za su ja hankalin kowa da kowa. Lv Yating na da fuska kamar ta yara amma a nutse da sanyin hali.

An haife ta a garin Jingdezhen a shekara ta 1993. Ba wai ita ce ta gaji fasahar harhada launukan kayan fadi-ka-mutu na Linglong ba, fasahar daya ce daga cikin abubuwan tarihi na al’adu da ake gada daga kakanni kakanni na kasar Sin, kuma ita ce shugabar wani kamfanin samar da kayan fadi-ka-mutu na wurin.

Shekaru tara da suka wuce, Lv Yating ta dawo daga kasar waje bayan kammala karatunta, kuma ta fara kasuwancinta a garin Jingdezhen.

Kayan fadi-ka-mutu na Linglong dake bukatar fasaha mai ban sha’awa, na daya daga cikin shahararrun fadi-ka-mutu na gargajiya guda hudu a garin Jingdezhen, amma saboda tsananin bukatar wannan fasaha, irin wannan nau'in kayan da ake samarwa a baya ba su da yawa, sabili da haka yana da matukar daraja. Lv Yating ta gaya mana cewa,

“Dalilin da ya sa ake samun karancin kayan fadi-ka-mutu shi ne, ana sassaka su a suffar cikakken jiki, sannan a cika shi da launuka, bayan haka kuma, a harba shi a cikin tukunyar, don haka da kyar ake iya samun irin wannan kaya mai inganci.”

A cewar Lv Yating, duk da haka halayen kayan fadi-ka-mutu a bayyane suke, ramukan auna jikinsu masu kama da sarari, wanda ba ya zubar da ruwa. Idan aka sanya shi a karkashin haske, to suna kama da kananan tagogi masu ba da haske kamar lu’u lu’u.

A ko da yaushe Lv Yating tana ba da shawarar warware matsaloli na kayan fadi-ka-mutu masu launukan shudi da fari na gargajiya, da ba da damar wannan tsohuwar fasaha ta shiga dubban gidaje, da kuma samar da ingantaccen kayan fadi-ka-mutu da zai dace da ma’aunin zamanin yanzu kan ma’anar kyan gani. Aikin cike launuka kan kayan fadi-ka-mutu na Linglong, shi ne mafi mahimmanci a cikin dukkanin ayyukan samar da kayan, wanda kuma ya kasance babban abin da Lv Yating ta mayar da hankali akai.

Bayan ta dawo kasar Sin daga kasar waje, ta fara bin malaminta domin koyon fasahar gargajiya. A cikin shekaru masu zuwa, ita da kungiyarta sun ci gaba da daidaita ma'auni, kuma sun gudanar da gwaje-gwajen harbi har sau sama da dari. Daga kayan fadi-ka-mutu mai launin fari zuwa na lu’u lu’u mai launin kore, sa’an nan kuma zuwa sabon nau’i mai launuka daban daban ... Lv Yating ta ce duk dagewa da ta yi ba wai kawai ya samo asali ne daga son wannan fasaha ta gargajiya da take yi ba ne kadai, har ma da jajircewar da ta samu wajen yin karatu a kasashen waje. Ta ce,

“Tsawon lokacin da na yi karatu a kasar waje, tabbas ya fadada tunani na sosai, inda na hadu da mutane iri-iri, da al'adu daban-daban, da hanyoyin tunani daban-daban, ko kuma ra'ayoyi daban-daban.”

A cewar Lv Yating, a hakika dai duk wadannan abubuwa sun yi mata tasiri a hankali a hankali. A matsayin ta na mai shugabancin kamfanin, tana bukatar zama mai budewa da hada kai. Yayin da take karatu a kasar waje, ta sami kwarewar yin tunani da na warware matsaloli bisa zaman kanta. Ta kara da cewa, tana bukata ta dauki alhakin kamfanin, tana kuma bukatar yin cikakken tsare-tsare don ci gaban kamfanin na dogon lokaci.

Yanzu, kungiyar Lv Yating ta cimma nasarar neman takardar ikon mallaka kan fasahar samar da kayan fadi-ka-mutu na Linglong, kuma ta kafa sabuwar alama. A karkashin jagorancinta, daukacin kungiyar masana’antar, tun daga tsofaffin masanan da suka yi aiki shekaru da yawa zuwa matasa, suna kan hanyar yin kirkire-kirkiren fasaha. Ta ce,

“Haka nan sakamakon kirkire-kirkire kan fasaha ne muka kai ga kafa alama daga baya. Kuma sakamakon ci gaba da kirkira da daidaita fasaha, za mu iya inganta samar da kaya bisa babban mataki.”

Yanzu, an sayar da kayayyakin da kamfanin Lv Yating ta kera ga kasashe da yankuna da dama, kuma ana amfani da su a matsayin farantin kasa wajen harkokin diflomasiyya. Lv Yating ta ce, a matsayinta na 'yar kasar Sin, tana alfahari da samun damar tsayawa kan dandalin kasa da kasa, da nuna fara'ar kayan fadi-ka-mutu na Linglong ga 'yan kasashen waje.

“Da muka je Japan don halartar wani nune-nune mun jawo hankulan baki da yawa, da masu ba da kayayyaki na kasashen waje, suna son kayan fadi-ka-mutu na Linglong sosai, ta yadda ba za su iya boye kaunarsu kan kayan ba.”

A cewar Lv Yating, suka zo suka tambaye su yadda suka kera kayan na Linglong? Me ya sa ba su taba ganin shi ba? A duk lokacin baje kolin, mutane suna zuwa don kara fahimtar kayayyakinsu. Lv Yating ta ce, me ya sa Sinawa ke iya kera kaya mai kyau kamar haka, amma sauran kasashe ba sa iya ba, hakan ya sa ta yi alhafari sosai a matsayinta na ‘yar kasar ta Sin.

Jingdezhen, wani tsohon gari ne mai tarihin shekaru dubu, sakamakon kyawawan al'adun tarihi da yake da su ne yake jawo hankalin matasa daga ko'ina cikin duniya, ba wai kawai yana ba su damar zama a nan ba ne, har ma ya samar musu wani dandamalin cimma burinsu na raya sana’o’i, da yin kirkire-kirkire, da ma nazarin makomarsu a nan gaba.

Yin kirkire-kirkire a yayin da ake kokarin gadar fasahar gargajiya, wannan ba kwarewar kasuwanci ce ta Lv Yating kadai ba, har ma da hanyar da za a bi wajen bunkasa fasahar kayan fadi-ka-mutu na Linglong a nan gaba. A matsayinta na matashiya, tana fatan daukar wani muhimmin aiki na ba da labari game da kayan fadi-ka-mutu na kasar Sin ga duniya, da kuma shigar da kayan fadi-ka-mutu na Linglong cikin gidajen al’ummun duniya.