logo

HAUSA

Isra’ila ba za ta dakatar da matakan soja ba kafin ta cimma burinta, in ji Netanyahu

2024-01-08 14:03:47 CMG

Alkaluman da hukumar lafiya ta zirin Gaza ta samar a jiya Lahadi sun shaida cewa, adadin wadanda suka halaka sakamakon rikicin da ya barke a tsakanin Palasdinu da Isra’ila a wannan karo, ya karu zuwa 22,835, a yayin da wasu 58,416 suka jikkata. A cewar hukumar, a cikin sa’o’i 24 da suka gabata, sojojin Isra’ila sun kaddamar da hare-hare har 12 a kan zirin Gaza, wadanda suka yi sanadiyyar mutuwar mutane 113, tare da jikkata wasu 250.

Jaridar The Times of Israel ta ba da rahoton cewa, a jiya firaministan kasar Benjamin Netanyahu ya bayyana cewa, kasarsa ba za ta dakatar da matakan soja a kan mayakan kungiyar Hamas a zirin Gaza ba, har sai ta cimma cikakken burinta.

A wannan rana kuma, sarki Abdullah II Bin Hussein na kasar Jordan ya gana da sakataren harkokin wajen kasar Amurka Antony Blinken da ke ziyara a kasar, inda ya jaddada cewa, daidaita batun Palasdinu shi ne sharadin tabbatar da kwanciyar hankalin shiyyar, kuma “shirin samar da kasashe biyu” yana da muhimmanci wajen daidaita batun.

Haka kuma a wannan rana, shi ma sarkin Tamim Bin Hamad Al Thani na kasar Qatar ya gana da Antony Blinken lokacin da ya kai masa ziyara a birnin Doha, babban birnin kasar, inda ya bayyana cewa, dole ne a hanzarta tsagaita bude wuta a zirin Gaza, tare da ba da kariya ga fararen hula da kuma tabbatar da samar da isassun kayayyakin agaji a dukkanin sassan zirin Gaza kuma mai dorewa. (Lubabatu)