logo

HAUSA

Cin abinci yadda ya kamata a farkon lokacin samun ciki yana rage barazanar kamuwa da ciwon sukari na lokacin goyon ciki

2024-01-08 08:07:41 CMG Hausa

 

Matsalar kiba, mummunan dalili ne dake sa masu juna biyu su kamu da ciwon sukari yayin da suke da ciki. Jami’ar Turku ta kasar Finland ta bayyana a kwanan baya cewa, masu nazari daga jami’ar sun shiga wani bincike, wanda ya nuna cewa, al’adar cin abinci tana yin tasiri kan kamuwa da matsalar kiba, da kuma kamuwa da ciwon sukari a lokacin samun ciki. Idan an mai da hankali kan cin abinci ta hanyar da ta dace a farkon lokacin samun ciki, to, za a rage barazanar kamuwa da ciwon sukari na lokacin goyon ciki.

Masu nazarin sun yi bincike kan alakar da ke tsakanin yadda masu juna biyu dari 3 da 51, wadanda nauyinsu ya wuce misali, ko kuma suke fama da matsalar kiba, da kuma kamuwa da ciwon sukari na lokacin samun ciki. Masu nazarin sun raba wadannan masu juna biyun zuwa rukunoni guda 2, bisa abubuwan da suka rubuta dangane da yadda suke cin abinci a farkon lokacin samun ciki. A rukuni na A, masu juna biyun suna cin abinci yadda ya kamata. A rukuni na B kuwa, ba sa cin abinci ta hanyar da ta dace. Masu juna biyun daga rukuni na A sun saba da cin kayayyakin lambu, ‘ya’yan itatuwa, burodin bakar alkama, kifi, naman tsuntsayen kiwo da kwai. Masu juna biyu daga rukuni na B kuwa su kan ci aiskirim, kayayyakin zaki, sukari, cakulan, fashewar shinkafa, soyayyen dankali da abin sha mai zaki.

Sakamakon nazarin ya nuna cewa, yadda ake cin abinci ta hanyar da ta dace a farkon lokacin samun ciki, yana rage barazanar kamuwa da ciwon sukari na lokacin goyon ciki. Idan aka shigar da kiba fiye da yadda ake bukata cikin jiki, to, za a samu karin kumburin jiki, ta yadda za a kara fuskantar barazanar kamuwa da ciwon sukari na lokacin samun ciki.

To ko ta yaya za a magance hakan? Madam Zhang Chuji, likita ce da ke aiki a asibitin Tiantan na Beijing, ta kuma yi mana karin bayani da cewa, kamata ya yi masu juna biyu su kara cin kayayyakin lambu, ‘ya’yan itatuwa, kayayyakin alkama da abinci masu cike da kitse mai inganci, wadanda suke iya rage kumburi a jikin dan Adam, domin ta haka ne za a rage barazanar kamuwa da ciwon sukari na lokacin goyon ciki. Ta ce mata masu kiba, ko wadanda nauyinsu ya wuce misali kafin sun samu ciki, sun fi cin gajiyar al’adar cin abinci ta hanyar da ta dace. (Tasallah Yuan)