logo

HAUSA

UNICEF: Yaran Gaza na fama da yunwa da matsalar damuwa

2024-01-07 16:02:55 CMG Hausa

Tun bayan barkewar rikici tsakanin Palastinu da Isra’ila, a halin yanzu yara dake zirin Gaza na fama da matsalar jin kai kamar yunwa da matsalar damuwa.

Jiya Asabar kakakin asusun kula da kananan yara na MDD ko UNICEF a takaice, Tess Ingram ta bayyana cewa, sakamakon binciken da aka yi ya nuna cewa, adadi mai yawa na yara a zirin Gaza suna fama da wahalhalu iri daban daban kamar su yunwa da rashin muhalli da kuma tabin  hankali. Sakamakon binciken ya yi nuni da cewa, yara ‘yan kasa da shekaru biyu kusan kaso 90 cikin dari, wato sama da dubu 130 ba su iya samun abincin da suke bukata ba. A sa’i daya kuma, tasirin rikice-rikicen kan lafiyar kwakwalwar yaran Gaza yana da matukar damuwa, da dama na fama da matsalar damuwa.

A cewar wani rahoto da gidan talabijin na Aljazeera ya watsa a jiya, ofishin kula da ayyukan jin kai na MDD ya bayyana cewa, makarantu da dama sun lalace saboda tashe-tashen hankula, kuma kusan kashi 90 cikin 100 na gine-ginen makarantu a zirin Gaza sun zama mafaka ga 'yan gudun hijira. Dalibai da dama sun rasa matsugunansu a zirin Gaza tun bayan barkewar wannan rikici, Ya zuwa yanzu rikicin ya shafi karatun dalibai sama da dubu 400 a zirin Gaza. (Jamila)