logo

HAUSA

Wani gidan abinci mallakin dan kasar Sin ya rabar da kayan masarufi ga marayu da masu karamin karfi a Kano

2024-01-07 15:26:52 CMG HAUSA

 

Katafaren gidan abinci na Red China Restaurant dake jihar Kano a arewacin Najeriya, mallakin wani dan kasuwar kasar Sin ya rabar da kayayyakin masarufi ga sama da mutane dari uku a jihar Kano, a wani mataki na rage masu radadin rayuwa da suke fuskanta.

Mutanen da suka amfana sun hada da Marayu da Masu bukata ta musamman da wadanda suke da rangwamen karfi, kuma an rabar da kayan ne a wurare daban daban dake cikin birnin Kano.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.