logo

HAUSA

An kama tsohon ministan makamashin Nijar tare da tusa keyarsa gidan kason birnin Yamai

2024-01-06 17:22:21 CMG Hausa

Bayan kwashe fiye da watanni hudu a kasashen ketare, shugaban jam’iyyar MPR-Kishin Kasa, Ibrahim Yacouba, kuma tsohon ministan makamashi cikin gwamnatin tsohon shugaban kasar Nijar Mohamed Bazoum ya shiga hannun jami’an tsaro a jiya ranar 5 ga watan Janairun shekarar 2024.

Daga birnin Yamai, abokin aikinmu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto.

 

A lokacin da aka yi juyin mulkin ranar 26 ga watan Yulin shekarar 2023 a Nijar, Ibrahim Yacouba na cikin rangadin aiki a kasashen waje. Daga can ne tsohon ministan ya soki lamarin juyin mulkin Abdourahamane Tiani da babbar murya da goyon bayan matakin karfin soja na kungiyar CEDEAO domin maido da tsohon shugaban kasa Mohamed Bazoum kan mulki. Furucin da ya janyo masa bakin jini ga yawancin ‘yan kasar Nijar. Haka kuma Ibrahim Yacouba na daga cikin jerin sunayen tsoffin mambobin gwamnatin faraminista Ouhoumoudou Mahamadou da sabbin hukumomin soja na CNSP suka ba da sammacinsu bisa laifin cin amanar kasa da salwantar da dukiyar kasa. Sai dai, kamar yadda malam bahaushe ke cewa, gida ta fi daji. Ibrahim Yacouba ya dawo birnin Yamai a ranar Alhamis da dadare, tare da shiga hannun jami’an tsaro na jandarma da suka tsare shi a tsawon kwana guda a ofishinsu na bincike, sannan kuma aka tusa keyarsa gidan yarin da ke birnin Yamai a ranar Jumma’a. A halin yanzu dai ba’a san laifuffukan da ake tuhumar shugaban jam’iyyar MPR-Kishin Kasa ba. Tsohon ministan makamashi ya iske a gidan kason tsohon wakilin shugaban kasa na musamman Foumakoye Gado kuma shugaban jam’iyyar PNDS-Tarayya tsofuwar jam’iyya mai mulki.

Tun lokacin da aka kafa hukumar yaki da cin hanci da yiwa dukiyar kasa zagon kasa ta COLDEFF ake ganin cewa, tsoffin shugabannin kasa da manyan jami’an gwamnati a lokacin mulkin Issoufou Mahamadou da Bazoum Mohamed za su amsa kiran wannan hukuma ba da jimawa ba.

Mamane Ada, sashen hausa na CRI daga Yamai a jamhuriyar Nijar.