Iran ta kama mutane 11 da ake zargi da hannu kan tagwayen hare-haren bam da aka kai a Kerman
2024-01-06 16:25:18 CMG Hausa
Ma'aikatar leken asiri ta kasar Iran ta sanar a jiya Jumma'a cewa, ta kama mutane 11 a larduna shida na kasar, da ake zargin suna da hannu a munanan hare-haren bama-bamai guda biyu da aka kai lardin Kerman da ke kudu maso gabashin kasar.
A cikin wata sanarwa da ma'aikatar ta wallafa a shafinta na yanar gizo, ta yi Allah wadai da harin ta'addanci da ya afku a kusa da kabarin Janar din sojan kasar Qassem Soleimani a birnin Kerman a ranar Larabar da ta gabata, harin da ya yi sanadiyar mutuwar a kalla mutane 89 tare da jikkata wasu 280.
Sanarwar ta bayyana cewa, jami'an leken asirin kasar sun yi nasarar zakulo 'yan ta'addar IS jim kadan bayan harin tare da hada kai da sauran sassan jami'an tsaro da na 'yan sanda, wajen zakulo wasu da ake zargi da taimakawa maharan.
Ta kara da cewa, daya daga cikin 'yan kunar bakin waken biyu, dan kasar Tajikistan ne, tana mai cewa, har yanzu ba a tantance ko wane ne dayan ba.(Ibrahim)