logo

HAUSA

Babban jami’in jin kai na MDD ya yi kira da a dauki matakin dakatar da yaki a Sudan

2024-01-05 10:43:59 CMG Hausa

Mataimakin sakatare-janar na Majalisar Dinkin Duniya mai kula da ayyukan jin kai Martin Griffiths a ranar Alhamis ya yi kira da a dauki matakin dakatar da yaki a Sudan.

Jami’in ya yi gargadin cewa, a yanzu da rikici ke kara ta’azzara a jihar Aj Jazirah na kasar, lamarin jin kai na kara tabarbarewa.

Kusan mutane miliyan 25 ne za su bukaci agajin jin kai a shekarar 2024 a kasar ta Sudan. To sai dai karuwar tashe-tashen hankula zai sanya agajin jin kai ba zai kai ga akasarin su ba.

Martin Griffiths ya kara da cewa, rikicin dake kara kamari a Sudan shi ma yana kawo cikas ga zaman lafiyar yankin, yayin da yakin ya haifar da matsalar gudun hijira mafi girma a duniya, wanda ya raba mutane sama da miliyan 7 barin matsugunansu kuma miliyan 1.4 daga cikinsu suka tsallaka zuwa kasashe makwabta da tuni suka karbi dimbin ’yan gudun hijira.

Yakin ya barke ne a watan Afrilun 2023 tsakanin sojojin Sudan da kuma dakarun sa-kai na RSF. (Muhammed Yahaya)