Bashin Amurka ya kai sabon matsayi wanda ke barazana ga tattalin arzikin kasar
2024-01-05 10:50:12 CMG Hausa
Sakamakon tasirin hauhawar bashin gwamnati, da karuwar farashin kayayyaki da sauran abubuwa, talakawa a kasar Amurka sun dauki nauyin tattalin arziki mai tsauri a bara.
Bayan shiga sabuwar shekara kuma, kididdigar da ma’aikatar kudi ta kasar ta sake bakanta rai Amurkawa, inda ya zuwa ranar 2 ga watan Janairun nan, yawan bashin da gwamnatin tarayyar Amurka ta ci ya kai fiye da triliyan 34, inda ya kai wannan adadi shekaru 5 kafin hasashen da ofishin kasafin kudi na majalisar dokokin Amurkan ya yi. Kuma hakan na nufin kowane Ba’amurke yana da bashin dalar a kalla dubu 100.
Masana sun yi hasashen cewa, bisa halin da ake ciki yanzu, gwamnatin Amurka za ta kara cin bashin dalar fiye da triliyan 2 a kowace shekara. Kuma la’akari da cewa jam’iyyu biyu na Amurka sun saba da juna kan batun kasafin kudi, kuma gwamnatin ba ta da shirin daukar mataki don magance matsalar bashin, kasashen waje sun yi hasashen cewa batun bashin Amurka zai ci gaba da tabarbarewa.
Asusun Peter G. Peterson, wato “Peter G. Peterson Foundation” ya bayyana cewa, bashi mai girma dake ci gaba da karuwa, yana kawo barazana sosai ga makomar tattalin arzikin Amurka.
A ganin sassan kasa da kasa, sakamakon dalar Amurka ita ce lamba ta farko wajen ajiyewa da biya, wato tsarin “Bashi mafi yawa da ba ya da iyaka” na Amurka, zai haddasa sauyawar kasuwar hada-hadar kudi ta kasa da kasa, har ma ya kawo illa ga tattalin arzikin duniya.
Sakatariyar baitul malin Amurka Janet L. Yellen, ta yi gargadin cewa, idan Amurka ta kasa biyan bashinta, hakan zai haddasa mummunan sakamako, wanda zai gurgunta tattalin arzikin kasa da ma na sauran sassan kasa da kasa. (Safiyah Ma)