logo

HAUSA

Gwamnatin jihar Sakkwato: An samu ci gaba mai yawa a aikin wanzar da tsaro a jihar

2024-01-05 09:06:53 CMG Hausa

Gwamnan jihar Sakkwato Alhaji Ahmed Aliyu ya tabbatar da cewa, yanzu an samu ci gaba mai yawa a aikin wanzar da tsaro a sassan jihar daban daban.

Gwamnan ya tabbatar da hakan ne lokacin da ya kai ziyarar jaje ga iyalan da ’yan uwan daruruwan mutanen da hare-haren ’yan bindiga ya yi sanadin rayuwarsu a yankin karamar hukumar Sabon Birni.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

Yankin karamar hukumar sabon birni ya kasance yankin da ya fi fuskantar kalubalen tsaro daga cikin kananan hukumomi 23 dake jihar Sakkwato.

Gwamna Ahmed Aliyu ya bukaci al’ummar yankin da su kwantar da hankalinsu, kasancewar hadin gwiwar jami’an tsaro sun ci karfi ’yan ta’addan dake yankin da ma sauran sassan jihar baki daya.

Ya nanata cewa gwamnatinsa ba za ta nuna gajiyawa ba wajen kare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar.

“Yaya ’yan uwana, al’ummar karamar hukumar mulki ta Sabon Birni da jihar Sakkwato baki daya, mu sani gwamnati ita kadai ba ta iya maganin tsaro ba, tsaron nan maganinsa yana hannunku. Ku ne za ku zo ku bayar da labaran sirri, ku fadi wadanda suka shigo baki, ku fadi wadanda suke cikinku, amma kuma suna yiwa ’yan ta’adda leken asiri. Ta wannan hanya ce kawai ake tabbatar da cewa a samar da tsaro a fadin wannan jiha tamu baki daya.”

Yayin wannan ziyarar dai gwamnan na jihar ta Sakkwato ya bayar da tallafin kayan abinci domin dai saukakawa al’ummar dake yankin, musamman wadanda suke zaune a wasu sansanoni da aka samar. (Garba Abdullahi Bagwai)