logo

HAUSA

IS ta yi ikirarin kai harin Kerman a Iran

2024-01-05 10:44:53 CMG Hausa

A ranar Alhamis ne kungiyar ta’addanci ta IS ta dauki alhakin tashin wasu munanan bama-bamai guda biyu a birnin Kerman dake kudu maso gabashin kasar Iran.

Kungiyar ta IS ta fitar da wata sanarwa cewa, ’yan kunar bakin wakenta guda biyu sun yi amfani da damarar bama-bamai a hare-haren guda biyu, a cewar kamfanin dillancin labarai na Iran IRNA.

A kalla mutane 84 ne suka mutu yayin da wasu 284 suka jikkata a ranar Laraba da ta gabata a wani tagwayen harin bama-bamai da aka kai a kusa da kabarin babban hafsan sojin Iran Qassem Soleimani dake Kerman a daidai lokacin da ake gudanar da taron tunawa da cika shekaru hudu da mutuwar Soliemani a wani harin da jirgin Amurka maras matuki ya kai.

An kashe Soleimani, daya daga cikin kwamandojin soji mafi karfi a Iran, a ranar 3 ga watan Janairu na shekarar 2020, kusa da filin jirgin sama na Bagadaza, a wani harin jirgin yaki maras matuki bisa umarnin Donald Trump, shugaban kasar Amurka na lokacin.

An binne shi a garinsa na Kerman, jana’izarsa ta samu halarcin miliyoyin mutane daga duk fadin kasar Iran. Kasar ta Iran ta yi Allah wadai da kisan a matsayin “ta’addancin kasar Amurka” tare da shan alwashin daukar fansa. (Muhammed Yahaya)