logo

HAUSA

Isra'ila ta sanar da dakatar da ayyukan soji a wasu sassan Rafah

2024-01-05 20:12:01 CMG Hausa

 

Rundunar sojin Isra'ila ta sanar da cewa, a bisa dalilai na jin kai za ta dakatar da ayyukan soji a gundumar Tel al-Sultan da ke birnin Rafah a zirin Gaza daga karfe 10 na safe zuwa karfe 2 na rana agogon wurin don bayar da damar kai kayayyaki.

Daga yau Jumma'a, za a rufe titin Salah al-Din, wanda ya taso daga arewa zuwa kudu a zirin Gaza, kana za a bude hanyar Rashid da ke gabar tekun Meditireniya. Daga karfe 9 na safe zuwa karfe 4 na yamma, mazauna arewacin Gaza na iya tafiya da kafa ko ta mota zuwa yankin kudanci.(Ibrahim)