logo

HAUSA

Rahoton MDD ya yi hasashen koma bayan tattalin arzikin duniya a 2024

2024-01-05 10:16:21 CMG Hausa

Rahoton nazari game da yanayin bunkasar tattalin arzikin duniya, da hasashen ci gaban sa na MDD na shekarar 2024, wanda aka fitar a jiya Alhamis, ya yi hasashen koma bayan tattalin arzikin duniya, daga kimanin kaso 2.7 bisa dari a 2023 zuwa 2.4 shekarar 2024.

Dalilan da rahoton ya yi hasashen za su haifar da koma bayan sun hada da raunin hada hadar cinikayyar duniya, da tsadar kudaden lamuni, da hauhawar basussuka, da karancin zuba jari, da karuwar zaman dar dar a wasu sassan kasa da kasa.

Kaza lika, rahoton ya ce akwai yiwuwar a samu koma bayan ci gaban tattalin arziki a kasashe masu ci gaba da dama, musamman Amurka, wadda rahoton ya yi hasashen za ta gamu da koma baya a 2024, sakamakon hauhawar farashin kudin ruwa, da raguwar kashe kudade tsakanin al’umma da kuma raunin kasuwar kwadago.

Har ila yau, rahoton ya ce ci gaban tattalin arziki na gajeren zango, tsakanin tarin kasashe masu tasowa, musamman na gabashin Asiya, da yammacin Asiya, da Latin Amurka da Karebiya, shi ma zai gamu da koma baya, sakamakon matsi a fannin sharuddan samar da kudade, da koma bayan tsarin kasafin kasashen yankunan, da tafiyar hawainiya ta fuskar bukatun waje.

Daga karshe, rahoton ya ce kasashe masu raunin samun kudaden shiga, da marasa karfi, na fuskantar karin gibi tsakanin kudaden dake shiga da wadanda ke fita daga gare su, da kuma rashin tabbas ta fuskar dorewar biyan basussuka.  (Saminu Alhassan)