logo

HAUSA

Akwai bukatar fadada masana’antun harkokin wasanni a kasar Sin

2024-01-04 15:06:07 CRI

A baya bayan nan, al’ummar kasar Sin na kara rungumar harkokin wasanni yadda ya kamata, wanda hakan ke nuni ga bukatar da ake da ita ta fadada masana’antun samar da kayayyaki, da hidimomin da ake bukata domin kara raya fannin, tun daga mataki na farko har zuwa na kwararrun masu shiga harkokin wasanni.

Sauyi daga samar da kayayyaki zuwa samar da hidimomi

Wani abu da aka lura da shi yayin baje kolin harkokin wasanni na shekarar 2023 da ya gabata, shi ne yadda ake samun karuwar harkokin kasuwanci na gida masu yawan gaske, wadanda ke sauya alkibla daga kera kayayyakin amfani yayin wasanni, zuwa cikakkun hidimomin da suka shafi fannin na wasanni ga masu bukata, tun daga makarantu har zuwa kungiyoyi da al’ummu. Akwai kuma karin masu samar da hidimomi ga daidaikun mutane, da sauran masu bukatu daban daban.

Da yake tsokaci game da hakan, mataimakin shugaba, kuma babban sakataren gamayyar kungiyoyin shirya wasanni na kasar Sin Luo Jie ya ce "Motsa jiki bukata ce ta mutane daban daban, don haka akwai babbar kasuwa a fannin. Akwai masu bukatar abubuwa domin bukatunsu su kadai, wanda hakan ke ingiza karsashin kasuwar. Kamfanoni da dama na gaggauta sauya akalar su da fadada sauye sauye, ta yadda za su kai ga samun karin kasuwanni".

Gasannin da ake shiryawa a birane da kauyuka na karuwa

A shekarar 2023, an ga yadda karin al’ummun kasar Sin ke shiga wasan gudun dogon zango ko “marathons”. A tsakanin watan Janairu zuwa Yuni na shekarar, an shirya irin wannan gudu har 133 a sassan kasar Sin. Kaza lika tsakanin ranaikun 25 da 26 ga watan Nuwambar shekarar, an gudanar da gudun “marathons” har sama da 20 a wurare daban daban na kasar.

Gudun “Beijing Marathon”, ya samu halartar sama da masu gudu 130,000, wadanda suka yi rajistar guraben cin kyautuka 30,000, inda masu gudu daga rukunoni daban daban suka shiga aka fafata da su ba tare da la’akari da kwarewa ba, kuma an kammala gudun na tsawon kilomita 42.195 cikin nasara.

Wannan karsashi na sha’awar wasan gudu ya yi tasiri ga tattalin arzikin kasar Sin. Ga misali, yayin tseren “Nanchang Marathon”, an samu harajin da ya kai yuan miliyan 125, kwatankwacin dala miliyan 17.6.

A cewar Li Xiaoping, darakta a hukumar wasanni ta lardin Jiangxi, "Gudanar da wasan tseren dogon zango ya zama wani jigo na raya tattalin arziki da zamantakewar al’umma a lardin Jiangxi".

Kaza lika, akwai manyan gasanni na kasa da kasa da ake shiryawa, kamar gasar wasannin jami’o’i ta “Chengdu Universiade”, da gasar wasannin Asiya ta Hangzhou, da gasar kwararru irin su “Chinese Super League” ko CSL ta kwallon kafa, da ta kwallon kwando wadda hukumar CBA ke shiryawa, dukkanin su na kara zaburar da ci gaban tattalin arzikin kasar.

Har ila yau, su ma gasannin ajin wadanda ba kwararru ba da ake shiryawa a yankunan karkarar kasar Sin suna samun nasarori.

Ga misali, gasar kwallon kafa ta "Cun Chao", wadda ke gudana a gundumar Rongjiang, ta lardin Guizhou na kudu maso yammacin kasar Sin, na ta samun karin karbuwa tun daga tsakiyar shekarar 2023. Rahotanni sun ce gasar ta hallara ‘yan kallo har sama da miliyan 2, inda a duk wasa akan samu dandazon jama’a a kalla 50,000. Haka za lika, akwai makamantan wannan gasa da ake shiryawa na wasannin kwallon kwado, da kwallon raga ta “volleyball”.

Game da haka, darakta a cibiyar bincike da samar da ci gaban masana’antar wasanni ta jami’ar Tsinghua Wang Xueli, ya ce "A birane ko a kauyuka, wasanni na taka muhimmiyar rawa. Wasanni na hade al’umma wuri guda, suna matso da al’ummun birane da kauyuka daban daban kusa da juna. Wannnan na nuni ga irin ci gaban da ake samu a fannin ci gaban kauyukan kasar Sin".

Wasanni da ake yi a budaddun wurare na samun karin tagomashi

A shekarar 2023, wasannin da ake gudanarwa a budaddun filaye na karuwa a kasar Sin. Tun daga wadanda ake yi a kan titunan birane har zuwa na sassan karkara, ana iya ganin masu wasanni daban daban na gudanar da wasannin su kamar su hawan tuddai da duwatsu, tsere ko gudu, da tseren kekuna.

A lardin Yunnan na kudu maso yammacin kasar Sin kadai, adadin mutane dake shiga irin wadannan wasanni a kalla sau daya a mako ya haura mutum miliyan 22, kamar yadda hukumar lura da harkokin wasanni ta lardin ta bayyana.

A cewar Huang Jin, jami’i a hukumar wasanni ta kasar Sin "Hakan abun sha’awa ne, dake nuna yadda jama’a ke kara son motsa jiki da kare lafiyar tunani, kana suna kara bayyana burin su na cudanya da halittun dake kewaye da su. Kaza lika, hakan na nuna kyautatuwar kayayyakin da ake bukata wajen gudanar da harkokin wasanni".

Wani rahoto da aka fitar game da fannin wasannin da ake gudanarwa a budaddun wurare na kasar Sin na 2022-2023, ya nuna yadda aka samu karuwar kaso 79 bisa dari na shigar mutane cikin irin wadannan nau’o’in wasanni a rabin farko na shekarar 2023, idan an kwatanta da makamancin lokacin na shekarar 2022, karuwar da ta kai kaso 221 bisa dari idan an kwatanta da makamancin lokacin na shekarar 2019.

Bugu da kari, wani shirin aiki da aka tanada domin bunkasa samarwa, da kyautata filayen wasanni da ake gudanarwa a budaddun wurare na Sin na shekarar 2023-2025, ya kunshi hasashen kasha kudade da yawan su ya kai yuan tiriliyan 3 a fannin na wasannin da ake gudanarwa a budaddun wurare a kasar Sin nan zuwa shekarar 2025.

Shirin wanda hukumar samar da ci gaba, da aiwatar da sauye sauye ta Sin ta fitar a watan Oktoba, da hadin gwiwar babbar hukumar wasanni ta kasar da sauran sassa masu ruwa da tsaki, ya nuna fatan da ake da shi na tallafawa, wajen gudanar da ayyukan raya wasanni da ake yi a budaddun wurare, da gabatarwa jama’a manyan gasanni masu nasaba, da shigar da dabaru daban daban na ingiza ci gaban nau’o’in wasannin", kamar dai yadda Yang Xuedong, darakta a sashen raya tattalin arziki na babbar hukumar wasanni ta kasar Sin ya bayyana.