Kasashen Afirka na fadada cudanya da kasar Sin a fannoni daban daban
2024-01-04 15:43:34 CMG Hausa
Ga duk mai bibiyar harkokin da suka shafi cudanyar kasar Sin da kasashen Afirka musamman a shekarar 2023 da ta gabata, ba zai rasa ganin muhimman nasarori da sassan biyu suka cimma a fannin yaukaka dangankata, da cimma moriya tare ba.
Karkashin dandalin bunkasa hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka na FOCAC, da manufofin bunkasa ci gaban duniya, da na wanzar da tsaron kasa da kasa, da shawarar wayewar kan duniya, tare da karfafa matakan gina shawarar “ziri daya da hanya daya” ko BRI da Sin ta gabatar, an kai ga cimma manyan nasarori masu fa’idar gaske.
A baya-bayan nan, mun ga yadda hadin gwiwa tsakanin Sin da Habasha ke kara samun tagomashi a fannonin cinikayya, da zuba jari, da samar da manyan ababen more rayuwa, da noma da sadarwa. Sauran sun hada da fannin raya al’adu, da ilimi, da musaya tsakanin al’ummun sassan biyu da sauransu, wanda hakan ya haifar da moriya mai tarin yawa ga jama’ar kasashen biyu.
A bana kuma, ana sa ran aiwatar da matakai daban daban na daga matsayin dangantakar Sin da Habasha bisa mutunta juna, da fadada tattaunawa tsakanin jami’ai, ta yadda za a gudu tare a tsira tare.
Baya ga Habasha, ita ma kasar Tunisiya ta karbi bakuncin taron musaya a fannin wayewar kai na hadin gwiwa da kasar Sin, taron da ya gudana a farkon makon jiya a birnin Tunis.
An jiyo wasu daga manyan baki mahalarta taron na bayyana shi a matsayin dama ta musaya, da tattaunawa game da wayewar kan Sin da Tunisiya, wanda zai ingiza ci gaban bai daya, da wadata tsakanin kasashen biyu.
Kaza lika, wasu masharhanta na ganin shawarar Sin ta ingiza wayewar kan duniya, wadda ke fatan ganin an samu zaman jituwa da koyi daga nasarorin juna tsakanin wayewar kai daban daban, karkashin taruka masu kama da irin wanda aka shirya a birnin Tunis, zai taimaka matuka wajen bunkasa wayewar kan daukacin bil adama.
Yayin da Sin da Tunisiya ke samun karin tagomashi a fannin bunkasa dangantaka, da yadda Sin din ke fadada cudanya da Habasha, sauran kasashen Afirka ma na bin wannan tafarki, na cin gajiya, tare kasa mafi girma a jerin kasashe masu tasowa wato kasar Sin, musamman a shekarun baya bayan nan.
Fatan dai shi ne kamar yadda aka raya kyakkyawar dangantaka tsakanin kasashen Afirka da Sin a shekarar 2023 da ta shude, hakan zai dore a bana wato shekarar 2024, zuwa shekaru da dama a nan gaba, ta yadda tafiya tsakanin Sin da kawayenta kasashe masu tasowa za ta dore har abada. (Saminu Alhassan)