logo

HAUSA

Harin ababen fashewa ya hallaka Iraniyawa 95 a wata makabarta dake kudu maso gabashin kasar

2024-01-04 09:59:51 CMG Hausa

Rahotanni daga kafofin watsa labarai na kasar Iran, sun tabbatar da rasuwar mutane a kalla 95, sakamakon tashin wasu ababen fashewa guda biyu, lokacin da dandazon mutane ke taron cika shekaru 4, da rasuwar babban jami’in sojin kasar Janar Qassem Soleimani, wanda wani harin jirgi maras matuki na Amurka ya hallaka.

Mutanen sun gamu da ajalin su ne a jiya Laraba, a cikin makabartar da aka binne Janar Soleimani, wadda ke birnin Keman na kudu maso gabashin kasar. Rahotanni sun ce baya ga wadanda suka rasu, akwai kuma karin sama da mutum 210 da suka jikkata.

Tuni dai mahukuntan Iran suka ayyana yau Alhamis a matsayin ranar makoki ta kasa. Kaza lika, babban shugaban addini na kasar Ali Khamenei, ya ce wadanda suka kitsa harin za su dandana kudar su.

Har ila yau, shi ma shugaban kasar Iran Ebrahim Raisi, ya ce ko shakka babu wadanda suka aikata wannan ta’asa matsorata ne, kuma gwamnati za ta zakulo su tare da tabbatar da an hukunta su.

Jami’an Amurka sun ce Amurka da kawar ta Isra’ila, ba su da hannu cikin aukuwar harin. A daya bangaren kuma, MDD da tarayyar Turai, da kasashen duniya da dama, ciki har da Rasha, da Türkiye, da Jamus sun yi Allah wadai da harin.  (Saminu Alhassan)