logo

HAUSA

Gwamnatin tarayyar Najeriya za ta hada hannu da jihar Jigawa wajen kammala babban aikin samar da ruwa a birnin Dutse

2024-01-04 09:06:04 CMG Hausa

Wata tawagar kwararru daga ma’aikatar albarkatun ruwa ta tarayyar Najeriya ta isa birnin Dutse, fadar gwamnatin jihar Jigawa domin nazarin hanyoyin da za a bi wajen tabbatar da kammalawar aikin samar da ruwa a birnin wanda aka fara tun a shekarar 1999.

Tawagar wadda ke karkashin jagorancin mataimakin daraktan samar da ruwa da tsaftar muhalli a birane na ma’aikatar Injiniya Abu Hassan ta ziyarci jihar ne bisa umarnin ministan ruwa Farfesa Joseph Utsev.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

A lokaci da suka ziyarci gidan gwamnatin jihar domin ganawa da gwamna Umar Namadi, jagoran tawagar Injiniya Abu Hassan ya ce, daga cikin abubuwan da za su duba shi ne ainihin cibiyar da aka tsara wajen samar da ruwa da kuma irin na’urorin da aka tanada domin aikin tunkudo ruwan cikin gari.

Ya ce, za su yi wannan aiki ne bisa hadin gwiwa da injiniyoyin da tun farko aikin ke hannunsu wanda kuma suke karkashin gwamnatin jihar.

“Babban aikin samar da ruwa na birnin Dutse yana cikin jerin ayyukan da za a gudanar a kasafin kudin bana na ma’aikatar albarkatun ruwa ta tarayya, kuma muna sane da kokarin da gwamna yake yi wajen tabbatar da ganin ya samar da kudade wajen aikin kari a kan wanda ma’aikatar ruwan ta samar.”

A jawabinsa gwamnan jihar Jigawa Alhaji Umar Namadi ya shaidawa tawagar ma’aikatar ruwan ta tarayya cewa, yana daga cikin burinsa tabbatar da samar da wadataccen ruwa a birnin Dutse.

“Gwamnatin jihar Jigawa ta dora muhimmancin gaske a kan wannan aiki, haka shi ma shugaban kasa ya nuna mun damuwarsa sosai a kan aikin, a saboda haka ina tabbatar muku cewa, ba za mu gajiya ba har sai hakanmu ya cimma ruwa.”

Shi dai wannan aiki na samar da ruwa kamar yadda masana suka yi hasashe, idan dai an kammala shi zai kawo karshen matsalar ruwa a birnin Dutse da kewaye. (Garba Abdullahi Bagwai)