logo

HAUSA

Ukraine da Rasha sun yi musayar fursunoni

2024-01-04 10:09:39 CMG Hausa

Hukumar dake kula da harkokin fursunonin yaki na Ukraine, ya ce kasashen Ukraine da Rasha sun yi musayar fursunoni mafi girma tun bayan watan Fabrerun 2022.

Hukumar ta bayyana a jiya Laraba cewa, karkashin shirin, an saki ‘yan Ukraine 230, ciki har da fararen hula 6 da Rasha ta tsare.

Haka kuma wadanda aka sakin sun hada da jami’an sojin Ukraine da jami’an tsaron kasa da na tsaron iyakoki da ‘yan sanda.

Wannan shi ne karo na farko da aka yi musayar fursunoni tsakanin bangarorin biyu tun bayan watan Augustan bara.

Zuwa yanzu, an saki sama da al’ummar Ukraine 2,800 da aka tsare sanadiyyar rikicin kasar da Rasha, karkashin shirin musayar fursunoni. (Fa’iza Mustapha)