logo

HAUSA

Mutane a kalla 81 sun mutu yayin da 51 suka baci cikin kasa da sa’o’i 72 da girgizar kasa a Japan

2024-01-04 15:41:13 CMG Hausa

Zuwa yammacin yau Alhamis, adadin wadanda suka mutu sanadiyyar girgizar kasa a yankin Ishikawa dake tsakiyar Japan ya karu zuwa 81, yayin da wasu 51 suka bace. Har yanzu ana gudanar da aikin ceto, kwanaki 3 bayan jerin girgizar kasa mai karfin maki 7.6 ya aukawa yankin da kewayensa. (Fa’iza Mustapha)