logo

HAUSA

Kungiyar gwamnonin arewa ta tsakiyar Najeriya ta bayar da gudummawar naira miliyan 100 ga wadanda harin Filato ya shafa

2024-01-03 09:59:19 CMG Hausa

Kungiyar gwamnonin jihohin dake arewa ta tsakiyar Najeriya ta bayar da gudummawar naira miliyan 100 ga mutanen da harin jajiberin Kirsimeti ya shafa a wasu kananan hukumomi uku dake jihar Filato.

Kungiyar ta bayar da gudummawa ce jiya Talata 2 ga wata, lokacin da gwamnonin jihohin karkashin jagorancin shugaban kungiyar, kuma gwamnan jihar Nasarawa Abdullahi Sule suka kai ziyarar jaje ga takwaransu na jihar Filato Caleb Mutfwanga.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

A lokacin da yake jawabi ga manema labarai bayan ziyarar gani da ido da suka kai wasu sassan da al’amarin ya faru, gwamnan jihar ta Nasarawa, kuma shugaban kungiyar gwamnonin jihohin arewa ta tsakiyar Najeriya ya ce, sun bayar da wannan tallafi ne domin rage wahalhalun da wadanda suka tsira daga hare-haren ka iya fuskanta kasancewar dai harin ya yi sanadin asarar muhallan jama’a da dama bayan ga munanan raunuka da wasu suka ji.

Ya ce, babu shakka dai kungiyar tasu tana matukar damuwa bisa rigingimun addini da na kabilanci da ake yawan samu a jihar Filato wanda hakan yana matukar shafar zaman lafiya a shiyyar baki daya.

Gwamna Abdullahi Sule ya ci gaba da cewa, ziyarar tasu zuwa jihar ta Filato za ta karawa gwamnan jihar ta Filato kwarin gwiwar bin diddigin musabbabin rikicin, ta yadda za a hadu a karkashin kungiyar gwamnonin domin maganin faruwar irin hakan a nan gaba.

“Dukkanninmu nan ’yan jihar Filato ne, kuma ba za mu taba bari jihar ta ci gaba da kasancewa a irin wannan hali ba, nan ba da jimawa ba ma za mu gudanar da babban taron jihohin arewa ta tsakiya kuma daya daga cikin batutuwan da za a tattauna yayin taron dai shi ne sha’anin tsaro.”

A jawabinsa, gwamnan jihar Filato Mr Caleb Mutfwang bayyana godiyarsa ya yi bisa wannan ziyara ta jaje da suka kawo masa, inda ya tabbatar masu da cewa gwamnati na bakin kokarin kara hada kan daukacin kabilun dake jihar baki daya. (Garba Abdullahi Bagwai)