Airbus ya tura kwararru domin binciken hatsarin jirgin sama a Japan
2024-01-03 09:59:32 CMG Hausa
Kamfanin Airbus mai kera jiragen sama, ya sanar da tura wani ayarin kwararru da za su taimakawa hukumomi binciken musabbabin hatsarin da ya rutsa da daya daga cikin jiragensa samfurin A-350 da ya sayarwa Japan.
Kafar yada labarai ta NHK ta kasar Japan, ta ruwaito a jiya cewa, an tabbatar da mutuwar 5 daga cikin mutane 6 dake cikin jirgin sama na tsaron ruwan Japan da ya yi taho-mu-gama da wani jirgin fasinja a filin jirgin saman Haneda na Tokyo a jiya Talata.
A daya bangaren kuma, dukkan fasinjoji 367 da ma’aikatan jirgi 12 dake cikin jirgin fasinja na Japan, sun tsira da rayukansu yayin da jirgin ya kama da wuta bayan taho-mu-gamar da ya yi da wancan karamin jirgin tsaron ruwan kasar. (Fa’iza Mustapha)