Hamas ta dakatar da tattaunawa da Isra’ila bayan kisan wani shugabanta a Beirut
2024-01-03 09:38:18 CMG Hausa
Kungiyar Hamas ta sanar da dakatar da tattaunawar tsagaita bude wuta da Isra’ila, bayan wani harin Isra’ila a Lebanon ya yi sanadin mutuwar wani mataimakin shugaban kungiyar mai suna Saleh al-Arouri da yammacin jiya Talata.
Wata majiya daga Hamas ta bayyana cewa, kungiyar ta sanar da ‘yan uwanta a Qatar da Masar game da batun dakatar da tattaunawar. Qatar da Masar dai sun kasance masu shiga tsakani dangane da batun tsagaita bude wuta tsakanin kungiyar Hamas da Isra’ila.
Majiyar ta kara da cewa, Hamas ta yi watsi da duk wani batun yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Zirin Gaza yayin da Isra’ila ke kara kaimi wajen kai hare-hare da kitsa kisan shugabannin Falasdinu.
Da farko, majiyar ta bayyanawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, an kashe hidiman al-Arouri da dama yayin harin da Isra’ila ta kai kan ofishin Hamas dake wajen yankin kudancin birnin Lebanon na Beirut.
Sai dai, babu wani tsokaci da Isra’ila ta yi game da batun. (Fa’iza Mustapha)