logo

HAUSA

Girgizar kasar Japan ta hallaka mutum 64

2024-01-03 10:41:32 CMG Hausa

A kalla mutane 64 aka tabbatar da rasuwarsu, sakamakon girgizar kasa mai karfin maki 7.6, da ta auku a yankin Noto na gundumar Ishikawa dake tsakiyar kasar Japan da yammacin ranar Litinin. 

Mahukunta sun ce har zuwa yanzu ana ci gaba da aikin ceto, domin zakulo wadanda gine-gine suka fadawa, a gabar da yankin ke ci gaba da fuskantar kananan girgiza bayan babbar girgizar kasar da ta auku.

Kafafen watsa labarai na cikin gida sun ce kimamin gidaje 33,900 a Ishikawa na fama da rashin makamashi da ruwa. Kaza lika a birnin Wajima wanda ya fi fuskantar girgizar kasar, an yi gargadin samun ruwan sama mai karfin gaske a Larabar nan, tare da fargabar samun karuwar zaftarewar kasa.

Yayin taron manema labarai na rana rana da ake gudanarwa, a jiya Talata, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya gabatar da sakon ta’aziyya ga iyalan wadanda girgizar kasar ta rutsa da su, tare da fatan samun sauki ga wadanda suka jikkata. (Saminu Alhassan)