Faransa ta rufe ofishin jakadancin ta dake Nijar a hukumance
2024-01-03 10:39:19 CMG Hausa
Kasar Faransa ta bayyana rufe ofishin jakadancinta dake jamhuriyar Nijar har sai baba ta gani. Ma’aikatar lura da harkokin Turai da kasashen waje ta Faransa ce ta sanar da rufe ofishin a hukumance.
Wata sanarwar da ma’aikatar ta fitar ga manema labarai a jiya Talata, ta ce matakin ya biyo bayan wasu manyan kalubale da ofishin jakadancin na Faransa a Nijar ke fuskanta cikin watanni 5 da suka gabata, wanda ke tarnaki ga gudanar da ayyukan ofishin yadda ya kamata.
Ma’aikatar ta ce ofishin jakadancin na Faransa zai ci gaba da aiki daga kasar Faransa, tare da tuntubar ’yan Faransa mazauna Nijar, yayin da za a ci gaba da gudanar da ayyukan diflomasiyya ta sauran ofisoshin jakadancin kasar dake yankin.
Sakamakon tabarbarewar alakar diflomasiyya, Faransa ta dakatar da samar da biza, tare da kwashe ’yan kasarta dake Nijar, yayin da ita kuma Nijar ta rufe sararin samaniyarta ga dukkanin jiragen sama masu rajistar Faransa. (Saminu Alhassan)