logo

HAUSA

Hadin gwiwar kasashen BRICS yana da makoma mai haske

2024-01-03 10:17:22 CMG Hausa

Tun daga ranar 1 ga watan Janairun shekarar bana, kasashen Saudiya, Masar, hadaddiyar daular Larabawa, Iran, da Habasha, sun zama mambobin kasashen BRICS a hukumance, wanda hakan ke nufin cewa, yawan mambobin kasashen BRICS ya karu daga 5 zuwa 10.

Game da hakan, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Wang Wenbin ya sanar a jiya Talata cewa, matakin ya shaida hadin gwiwar kasashen BRICS yana da makoma mai haske.

Ya ce, “Muna da kwarin gwiwa sosai kan ci gaban hadin gwiwar kasashen BRICS a nan gaba.” Wang Wenbin ya bayyana hakan ne yayin da yake amsa tambayoyi masu nasaba da batun, a gun taron manema labarai na rana rana da ake gudanarwa.

Ya kuma kara da cewa, karfin hadin kan kasashen BRICS ya ci gaba da karuwa, haka ma karfin tasirinsu, wanda ya riga ya zama karfi mai kwanciyar hankali, da aminci a cikin harkokin kasa da kasa.

Wang Wenbin ya ce yawan mambobin kasashen BRICS ya habaka zuwa 10, matakin dake shaida yanayin hadin gwiwar kasashen BRICS yana da makoma mai haske. Kuma kasashen BRICS su yanke shawarar habaka yawan mambobinsu bisa bukatar kasashen da abun ya shafa, lamarin da ya dace da bukatun sabuwar kasuwa da burikan kasashe masu tasowa, da ci gaban tarihin duniya.

Wang Wenbin ya kara da cewa, “Za mu inganta hadin gwiwar kasashen BRICS don samun sabon sakamako tare.”(Safiyah Ma)