logo

HAUSA

Yadda kasar Sin ta shawo kan matsaloli ta hanyar neman zamanintarwa bisa goyon bayan al’ummarta

2024-01-03 08:05:11 CMG Hausa

Mun yi ban kwana da shekara ta 2023, wacce ta kasance shekarar farfadowa daga ibtila’in COVID-19, da tasirin yakin Rasha da Ukraine ga tallalin arzikin duniya, ga rikice-rikicen Gabas ta Tsakiya, musamman na baya-bayan nan tsakanin Isra’ila da Falsdinu, da gwagwarmayar shugabancin duniya tsakanin kasashen yamma da sauran kasashen duniya, da rikice-rikicen sauyin yanayi, da sauran batutuwan da suka mamaye kanun labarai a shekarar 2023. Yana da muhimmanci mu waiwayi ci gaban da bil'Adama ya samu ta hanyar hadin kai, da ci gaban sabbin fasahohi musamman na zamani, da yunkurin diflomasiyya, da binciken sararin samaniya da zamantakewa, wadanda suka ba da gudummawa ga kyakkyawar labarin ci gaba da burin bai daya na bil’Adama a shekarar bara, musamman ma yadda kasar Sin ta shawo kan wadannan matsaloli masu nasaba da ci gabanta a fakaice ta hanyar neman zamanintarwa bisa goyon bayan al’ummarta.

Shugaba Xi jinping, a cikin jawabinsa na murnar sabuwar shekara ya bayyana cewa, bana ce ta cika shekaru 75 da kafuwar Jamhuriyar Jama'ar Sin.

Ya yi kira da a himmatu wajen ci gaba da zamanintar da kasar Sin gaba daya, da cikakken aiki da aminci ga sabon tsarin falsafar ci gaba daga dukkan bangarori, da gaggauta gina sabon tsarin raya kasa, da sa kaimi ga samun ci gaba mai inganci, da kiyaye tsaro, tare da yin kokari wajen karfafa yunkurin farfado da tattalin arziki, da samun ci gaban tattalin arziki mai dorewa. 

Xi ya jaddada bukatar zurfafa yin gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje, da kara karfin amincewar jama'a kan samun ci gaba, da sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arziki, da kara yin kokari wajen bunkasa ilimi, da ciyar da kimiyya da fasaha gaba, da raya hazaka.

A taron kolin tattalin arzikin kasar Sin da aka gudanar a ranakun 11 da 12 ga watar Disambar shekarar da ta shude a nan birnin Beijing, shugabannin kasar Sin sun yanke shawarwari kan muhimman batutuwan da suka shafi harkokin tattalin arziki a wannan shekarar 2024. A gun taron, an bayyana cewa, tattalin arzikin kasar Sin ya samu farfadowa, tare da samun ci gaba mai inganci. A dunkule, yanayi mai kyau ya zarce kalubaloli game da ci gaban kasar Sin, kuma tushen tsarin farfado da tattalin arziki da kyakkyawan hangen nesa na dogon lokaci bai canza ba.

A duk halin da ake ciki dai, kasar Sin za ta yi kokarinta wajen samar da tsare-tsare da kuma tuntuba da tattaunawa domin kara fahimtar muradun bai daya. Ba za ta nemi kasashen duniya da su rarrabu ba, akasin haka, za ta kiyaye ingancin tsarin samar da kayayyaki na duniya da sunan kyautata jin dadin jama'a kan karin kariyar ga kasashen duniya.

Har ila yau a cikin jawabin shugaba Xi Jinping, ya yi karin haske kan kudurin kasar Sin na ciyar da zamanantar da kasar Sin gaba, da samar da ingantacciyar rayuwa ga jama'a, da kokarin ganin duniya ta zama wuri mafi kyau ga kowa a shekarar 2024. (Muhammed Yahaya, Saminu Alhassan, Sanusi Chen)