logo

HAUSA

Mutane 73 sun mutu sakamakon fashewar bama-bamai a Kerman na Iran

2024-01-03 21:24:11 CMG Hausa

Kamfanin dillancin labaru na Fars na kasar Iran ya bayar da labari a yau cewa, ya zuwa yanzu, mutane 73 sun mutu a sakamakon tashin bama-bamai a birnin Kerman dake kasar Iran, kana mutane 173 sun ji rauni.

Mataimakin gwamnan jihar Kerman ya bayyana cewa, tashin bama-baman da ya auku sau biyu a birnin Kerman aikin ta’addanci ne. (Zainab)