logo

HAUSA

Hadin gwiwar Sin da Habasha na kara samun tagomashi a sassa daban daban

2024-01-02 10:06:42 CMG Hausa

Jakadan kasar Sin a kasar Habasha Zhao Zhiyuan, ya ce hadin gwiwar Sin da Habasha na kara samun tagomashi a sassa daban daban. Jakada Zhao wanda ya bayyana hakan cikin jawabinsa na sabuwar shekara, wanda aka wallafa a ranar Lahadi a jaridar kamfanin dillancin labarai ta Habasha ko EPA, ya ce kawance Sin da Habasha zai ci gaba da fadada a wannan sabuwar shekara.

Jakadan ya kara da cewa "Sassan biyu sun ci gaba da samun nasarori karkashin hadin gwiwar su a fannonin cinikayya, zuba jari, samar da ababen more rayuwa, noma, sadarwa, hada hadar kudade, da raya al’adu. Sauran fannonin sun hada da raya ilimi, da musaya tsakanin al’ummun su da dai sauran su, wanda hakan ke haifar da tarin alherai ga jama’ar kasashen biyu".

Zhao Zhiyuan ya ce a shekarar 2023, Sin da Habasha sun cimma nasarori masu ban mamaki karkashin hadin gwiwar su, kuma daga matsayin dangantakar su bisa matsayin koli daga dukkanin fannoni, zai yi matukar taimakawa burin su na zurfafa kawance, da daga matsayinsa zuwa wani sabon mataki. (Saminu Alhassan)