logo

HAUSA

Fasahar caccaka allurai cikin fatan jikin dan Adam don magani ta kasar Sin ta taimaka ga inganta lafiyar al’ummar Zimbabwe

2024-01-02 14:47:04 CMG Hausa

Shekarar da ta gabata ta 2023, shekaru 60 ke nan na irin gudanarwar ayyukan ba da agajin likitanci ga kasashen waje da sabuwar kasar Sin ta bayar. Daga cikin mambobin tawagar ba da agajin likitanci ga kasashen waje ta kasar Sin, akwai wasu likitoci masu amfani da fasahar caccaka allurai a fatan jikin dan Adam don magani wato Acupuncture, wadanda suka taimaka sosai ga inganta lafiyar dan Adam a kasashen Afirka. A shirinmu na yau, za mu kawo mu ku labaran tawagar ba da agajin likitanci ga kasashen waje ta kasar Sin dake gudanar da aikin likitancin acupuncture a kasar Zimbabwe, tare da sa kaimi ga bunkasuwar ayyukan likitanci na kasar.