logo

HAUSA

An nada tsohon shugaban ‘yan adawa a matsayin firaministan Chadi

2024-01-02 10:00:01 CMG Hausa

Shugaban gwamnatin rikon kwarya a Chadi Mahamat Idriss Deby Itno, ya nada tsohon shugaban ‘yan adawar kasar Succes Masra a matsayin sabon firaminista.

Masra, wanda ya jima yana adawa da gwamnatin Deby, ya tsere daga kasar a shekarar 2022, yayin da kasar ke tsaka da fama da kalubalen siyasa, kafin ya koma gida a watan Nuwamban shekarar da ta kare, sakamakon shiga tsakani da shugaban janhuriyar dimokaradiyyar Congo Felix Tshisekedi ya yi.

A watan da ta gabata, Masra, wanda ke jagorantar jam’iyyar “The Transformers political party”, ya goyi bayan gwamnati mai ci yayin kuri’un raba-gardama game da sabon kundin mulkin kasar.

Kafofin watsa labarai na Chadi sun rawaito cewa, nadin mista Masra na iya bude sabon bakin wanzar da sulhu, da zaman lafiya a kasar dake tsakiyar Afirka, wadda ta sha fama da matsalolin siyasa tun daga shekarar 2021, sakamakon rasuwar shugaban kasar na lokacin Idriss Deby Itno. Daga nan ne kuma dan sa Mahamat Idriss Deby Itno ya dare kujerar shugabancin gwamnatin rikon kwaryar kasar har zuwa yanzu. (Saminu Alhassan)