logo

HAUSA

Mutane Sama Da 90% Sun Nuna Damuwa Kan Yadda Kasafin Kudin Tsaron Amurka Da Japan Suka Kai Sabon Matsayi

2024-01-02 20:34:33 CMG Hausa

Kasafin kudin soja na kasashen Amurka da Japan na shekarar 2024 sun kai wani matsayi a tarihi, wanda ya zama abin damuwa a wannan yanayin rashin zaman lafiya. A cewar wani binciken jin ra'ayin jama'a na duniya da CGTN ya gudanar, kashi 93 bisa kashi 100 na wadanda suka ba da amsa ga binciken sun damu matuka, suna ganin cewa karuwar kudaden da Amurka da Japan ke kashewa a kan aikin soja ba bisa ka'ida ba, za ta kawo cikas ga zaman lafiya a yankin da kuma haifar da wani sabon zagaye na gasar makamai a gabashin Asiya da ma duniya baki daya.

Ko da yake ana zaman dar-dar, amma mutane na fatan zaman lafiya. A cikin binciken, kashi 95.6 bisa kashi 100 na wadanda suka ba da amsa ga binciken sun yi imanin cewa, bai kamata a tabbatar da tsaron wata kasa yayin da sauran kasashe ke fuskantar rashin tsaro ba, kuma bai kamata a tabbatar da tsaron wani yankin ta hanyar karfafa ko ma fadada sansanonin soja ba, don haka ya kamata ko wace kasa ta yi la'akari da matsalolin tsaro masu ma'ana na sauran kasashe yayin da suke neman nasu tsaron.

Haka zalika kashi 96.2 bisa kashi 100 na wadanda suka ba da amsa ga binciken sun ce, babu wanda yake yin nasara a yaki, kuma ya kamata dukkan kasashe su tsaya tsayin daka kan yin adawa da yake-yake, kuma su yi taka tsan-tsan kan duk wani yunkurin da zai kai ga yaki da kuma hadarin da ke tattare da yaki. Wajibi ne a inganta ginin duniya mai tsaro na gama-gari ga kowa da kowa. (Yahaya)