logo

HAUSA

Jarin Sin ya bunkasa sashen sabbin makamashi a Zimbabwe

2024-01-02 13:18:20 CMG Hausa

Minista mai lura da ma’aikatar tsoffin ’yan mazan jiya a kasar Zimbabwea Christopher Mutsvangwa, ya ce kwarewar kasar Sin a fannin raya fasahohin sabbin makamashi, da jarin da kasar ke zubawa a Zimbabwe na bunkasa nasarar kasar a fannin karkata zuwa makamashi maras gurbata muhalli.

Christopher Mutsvangwa, wanda ya bayyana hakan, yayin wata zantawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua a baya bayan nan, ya ce Zimbabwe na cin gajiya daga tasirin kasar Sin a fannin msana’antun kere-kere, inda kasar ke matsawa zuwa ga moriyar sabbin nau’o’in makamashi da duniya ke tunkaho da su, kuma Zimbabwe na maraba da karin jari daga Sin.

Daya daga bangarorin da Zimbabwe ke cin gajiyarsu shi ne jarin da kamfanonin Sin suka zuba, a fannin sarrafa ma’adanin “lithium” da ake hada batura da shi a kasar, wanda hakan ya kusantar da Zimbabwe ga cin gajiyar arzikin dake tattare da sashen.

Ministan ya kara da cewa, a watan Disamban da ya shude, gwamnatin Zimbabwe ta hana fitar da tsagwaron ma’adanin “lithium”, domin karfafa gwiwar zuba jari a fannin kayayyakin aikin sarrafa shi a cikin kasar. Kaza lika gwamnatin ta amince da manufar raya fannin sarrafa ma’adanin, da nufin fadada gajiyar da kasar ke ci daga gare shi. (Saminu Alhassan)